Yawan wadanda suka mutu saboda Kwalara sun karu a Haiti

Yawan mutanen da suka mutu da annobar cutar kwalara a kasar Haiti, ya zarta dari biyu da hamsin.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce, mutane dubu uku ne suka kamu da kwalarar, amma a yau Lahadi, mutane kalilan ne kawai aka gano sun kamu da cutar.

Tun farko an gano mutanen da aka tabbatar suna fama da aman da gudawa a Port-au-Prince, babban birnin kasar ta Haiti.

Amma a cewar likitoci, wannan ba ya nufin annobar ta bazu ne, saboda hudu daga cikin marasa lafiyar, sun je birnin ne daga wurin da annobar kwalarar ta fi kamari.