Gwamnatin Italiya ta jinkirta bude wani sabon wurin jibge shara

Gwamnatin Italiya ta jinkirta bude wani sabon wurin jibge shara, kusa da birnin Naples na kudancin kasar, bayan mazauna yankin sun kwashe makonni suna zanga-zanga.

A yanzu haka akwai fiye da ton dubu biyu na sharar da ba a kwashe ba, a kan titunan birnin na Naples.

A daren jiya an yi dauki-ba-dadi tsakanin daruruwan masu zanga-zanga da 'yan sanda, a garin Terzigno da ke kusa da sabon jujin da ake son kaddamarwa:

Rahotanni sun ce 'yan sanda shidda sun jikkata.

Firaministan Italiyar, Silvio Berlusconi, ya aika shugaban hukumar da ke kare fararen hula zuwa birnin na Naples, domin ganin yadda za a shawo kan lamarin.