A daren jiya Namadi Sambo ya gama ziyara a Birtaniya

A daren jiya ne mataimakin shugaban kasar Najeriya, Architect Mohammed Namadi Sambo ya kammala wata ziyarar kwanaki uku a Birtaniya.

A lokacin ziyarar tasa, mataimakin shugaban kasar Najeriyar ya gana da ministocin Birtaniya dake kula da nahiyar Africa da bayar da taimako ga kasashen waje.

Ministocin Birtaniyar sun tabbatar da cewa duk da irin matsin tattalin arzikin da suke fama da shi, za su ci gaba da karfafa dangantaka da Najeriya, musamman ta fuskar cinikayya.

Haka kuma Mataimakin shugaban Najeriyar ya gana da kungiyar 'yan kasuwa na Commonwealth, domin ganin ta yanda za su zo domin zuba jari a Najeriya, musamman ma wajen wajen bunkasa harkokin da suka shafi wutar lantarki da sufurin jirgin kasa.

Ganin irin matsalolin da Najeriya ke fuskanta ta fuskar tsaro Mataimakin Shugaban Najeriyar, ya jaddada cewa gwamnatin Najeriya za ta tabbatar da samar da tsaro a kasar.