Dalibai a Faransa zasu gudanar da jerin gwano

Zanga zangar dalibai a kasar Faransa
Image caption Dalibai a kasar Faransa zasu gudanar da wani jerin gwano domin nuna rashin jin dadinsu game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kara yawan shekarun ritaya

A yau ne dalibai a kasar Faransa ke shirin gudanar da wani jerin gwano a fadin kasar don nuna rashin jin dadin su ga matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kara yawan shekarun ajiye aiki ga ma'aikata.

Matsin lambar da akewa gwamnatin kasar dai ya dan ragu a 'yan kwanakin nan inda ma'aikatan wasu daga cikin matatun man kasar suka kada kuri'ar dakatar da yajin aikin da suka shiga.

Shugaba Nicholas Sarkozy na fatan kuri'a ta karshe da 'yan majalisun dokokin kasar zasu kada kan batun fansho a gobe laraba ka iya karya lagon 'yan adawa.

Yaje yajen aikin da ma'aikatan kasar faransa suka gudanar dai a baya ya gurgunta al'amura da dama a kasar