Kwalara ta fara ja da baya a Haiti

Kwalara ta fara ja da baya a Haiti
Image caption Fiye da mutane 250 ne suka rasu sakamakon cutar ta kwalara

Jami'an agajin da ke yaki da yaduwar cutar kwalara a kasar Haiti sun ce akwai alamun samun nasara a kokarin da ake na kawar da cutar.

Wata jami'ar kungiyar Save the Children ta shaida wa BBC cewa adadin masu kamuwa da cutar na raguwa.

Tace abinda ke kara mana kwarin gwiwa shi ne yadda aka yi saurin gano mutane biyar din da ke dauke da cutar a birnin Port au Prince tare da killacesu daga jama'a cikin gaggawa.

Fiye da mutane dari biyu da hamsin ne dai suka rasu sanadiyyar Kwalarar a Haiti, sai dai ma'aikatan agaji na aiki tukuru wurin samar da tsaftataccen ruwan sha domin rigakafin cutar.

Jami'ai suka ce cutar na barazana ga mutane miliyan daya da dubu dari uku, wadanda suka tsira daga mummunar girgizar kasar da ta afku a watan Janairu.

Rashin tsaftar muhalli na kara sanyasu cikin hadarin kamuwa da cutar, wacce ke yaduwa ta hanyar gurbataccen abinci da ruwan sha.