Za a hana mata shigar banza a Italiya

Za a hana mata shigar banza a Italiya
Image caption Irin wannan shiga dai ta zama ruwan dare a kasashen Turai da dama

Magajin garin Castellammare di Stabia, da ke yankin Naples a Italiya, na shirin hana mata sanya kananan tufafi wadanda ke bayyana tsiraici.

Garin dai shi ne na baya bayan nan a kasar ta Italiya, da ke kokarin amfani da wata sabuwar doka da ta basu damar hana sanya kayan da basu dace da al'ada ba.

Magajin gari Luigi Bobbio ya ce "dokar za ta taimaka wajen kyautata zamatakewa, da kuma fahimtar juna".

Duk wanda aka samu da laifi zai iya fuskantar tarar da ta kama daga dala (35) zuwa dala (696).

'Matakin ya dace'

"Babu abin da ya fito fili sosai" a dokar da magajin garin ke son aiwatarwa, a cewar wakilin BBC Duncan Kennedy da ke birnin Roma.

Abin da hakan ke nufi shine za a hana sanya duk wani tufafi da ke bayyana tsiraici, kama daga karamin siket da gajeren wando, alokacin da jama'a ke kaiwa da komowa a birnin.

Mista Bobbio, na jam'iyyar People of Freedom party, ya ce yana son tunkarar mutanen da ba su da da'a.

Har ila yau za'a kuma hana buga kwallon kafa a wuraren da jama'a ke zama, wadannan dokokin za su fara aiki ne idan har sun samu amincewar majalisar birnin wacce za ta kada kuri'a ranar Litinin. "Wannan matakin ya dace," a cewar wani malamin addinin kirista Don Paulo Cecere, ya kara da cewa hanya ce ta shawo kan karuwar barazanar cin zarafin da mata ke fuskanta".