Likitoci na kokarin shawo kan zazzabi mai zafi a Katsina

A Najeriya, likitoci a jihar Katsina suna can suna kokarin shawo kan wani ciwo, wanda mutane da daama suka yi imanin annoba ce ta wani zazzabi dake cigaba da hallaka jama'a.

Zazzabin, wanda wasu malaman asibiti a Katsina suka ce ba ya jin magani, ya sa asibitoci a kalla a babban birnin jihar sun cika makil da jama'a.

Saboda rashin gadaje a asibiti, wasu majiyantan, sai ma a gidajensu ma'aikaan kiwon lafiya suke iske su suna yi masu karin ruwa da ba su magunguna.