Kwalara ta kashe sama da mutane 1,500 a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 1,500 ne suka mutu a Najeriya a cikin wannan shekarar sanadiyyar cutar kwalara.

Majalisar ta ce yawan mutanen ya ninka adadin da gwamnatin kasar ta bayyana a watan Agustan daya gabata har sau hudu.

Bayanai daga Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa mutane 1,555 sun mutu sanadiyyar cutar tun daga watan Janairu a yayinda mutane 38,173 na jinya a asibitoci sanadiyyar cutar.

Martin Dawes, mai magana da yawun asusun bada tallafin ilimin yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ruwan sama da bakin kwarya da kuma ambaliya ya gurbata ruwan sha da kuma muhalli a karkara.

Ma'aikatar kula da lafiya a Najeriya a watan Agustan da ya gabata, ta ce barkewar cutar a kasar wacce tafi kamari a arewacin kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 352.

Har wa yau dai ma'aikatar ta yi gargadin cewar akwai barazanar barkewar cutar a kasar baki daya.