Kwalara ta hallaka mutane fiye da 1,500 a Nigeria

Kwalara
Image caption Kwalara

Jami'an kiwon lafiya na kasashen duniya sun ce mutane fiye da 1,500 ne suka rasa rayukansu a Nigeria a sakamakon cutar kwalara da ta barke a yankuna da dama na kasar.

Wannan adadi dai ya linka wanda gwamnatin kasar ta bayar har sau hudu.

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya watau UNICEF ya ce mutanen sun rasa rayukansu ne daga watan Janairu na bana a barnar da ita ce mafi muni cikin shekara da dama.

Cutar ta fi yin barna ne a arewacin kasar da ya fi fama da talauci.

Kamar yadda hukumar UNICEF ta bayyana, mutane kamar 38,173 ne suka kamu da wannan cuta.

Ana samun rashe rashen ne a yayin da wannan cuta ta ke ci gaba da addabar kasashe da dama a yankin Africa ta Yamma ciki kuwa har da jamhuriyar Benin.