Ma'aikatan PHCN sun yi zanga zanga a Lagos

Tashar wutar lantarki
Image caption Tashar wutar lantarki

Kungiyar ma'aikatan kamfanin samar da wutar lantarki ta Nigeria sun yin gudanar da wata wata zanga zanga a birin Lagos.

Ma'aikatan sun yi wannan zanga zanga ce domin nuna kin amincewa da shirin gwamnati na sakin ragamar samar da wutar lantarki ga kamfanoni masu zaman kansu. Kungiyar ma'aikatan kamfanin ta ce, akwai illa babba ga rayuwar talakawa da kuma harkokin tsaro in har gwamnati ta amince da hakan.