Zargin cin hanci a hukumar UEFA

Michel Platini
Image caption Hukumar UEFA ta musanta wannan zargi

Hukumar kula da kwallon kafa ta UEFA ta nemi a gabatar mata da shaidu kan zargin cinhanci game da yadda aka baiwa Ukraine da Poland damar daukar nauyin gasar cin kofin Turai a shekarar 2012.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Cyprus, Spyros Marangos, ya shaida wa wata jaridar Jamus cewa an yi magudi a kuri'ar da aka kada.

Zaben da aka yiwa Ukraine da Poland a watan Aprilun shekara ta 2007, a maimakon Italiya da kuma hadin guiwar kasashen Hungary da Croatia ya zo da bazata.

Jaridar ta Suddeutsche Zeitung, ta ce an baiwa wasu jami'ai cinhanci. Ta kara da cewa shugaban hukumar kwallon kafa ta Cyprus yana da shaidar cewa an baiwa jami'an UEFA biyar cin hancin Yuro miliyan 11.

UEFA ta yi watsi da kalaman nasa, tana mai neman a gabatar mata da shaidu nan da ranar Laraba mai zuwa.

A yanzu haka dai hukumar kula da kwallon kafa ta FIFA, tana gudanar da bincike kan zargin cin hanci da jaridar Sunday Times ta Burtaniya, ta yiwa wasu jami'an hukumar biyu.