An kusa kawarda cutar Polio a duniya

Yaki da cutar Polio
Image caption Masana kimiyya sunyi amannar cewar an kusa a kawadda cutar polio daga doran kasa biyo bayan wata sabuwar allurar rigakafin kamuwa da cutar da aka fara amfani da ita yanzu haka

Masana kimiyya sun ce sun yi amannar cewar nan bada jimawa bane za'a kawadda cutar nan ta Polio da ke addabar kananan yara.

Wani sabon magani da aka yi gwajinsa a kasashe biyu cikin kasashe hudu da yanzu haka cutar tayi kamari wadanda suka hada da Najeriya da kasar Indiya ya nuna raguwar cutar da kusan kashi casa'in da tara cikin dari.

Wani babban jami'in hukumar lafiya ta duniya ta WHO wato Dr. Bruce Aylward ya shaidawa BBC cewa sabuwar allurar rigakafin kamuwa da cutar, wata hanya ce da ake ganin zata kaiga kawadda cutar dungurungun.

A kasar India yawan yaran dake kamuwa da cutar sun ragu da kashi 90 cikin 100, yayinda a Najeriya an samu raguwar masu kamuwa da cutar da kashi 95 cikin 100.