An gano gawawwaki 13 a jihar Kuros Riba

Nigeria
Image caption Nigeria

Mahukunta a Jihar Kuros Riba, sun gano wasu gawawwaki da aka kona guda 13, bayan wani rikici da ake dangantawa da gonaki.

Rikicin kamar yadda mahukunta suka bayyana ya kuma haddasa kone-konen gidaje masu yawa da coci-coci.

Kakakin rundunar yan sanda na Jihar Kuros Riba, Mr Etim Dickson ya shaidawa manema labarai cewar an gano gawawwakin ne a wasu kauyuka biyu da ke gundumar Boki a Jihar.

Rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar lahadi inda ya kara rincabewa ranar litinin.

Tuni dai an tura 'yan sanda, kuma kakakin rundunar yan sandan ya ce tuni an maido da kwanciyar hankali.

An dai kafa dokar hana fitar dare a yankin da rikicin ya faru.