Bala'o'i da dama sun fada wa Indonesia

Tsunami ta haddasa ambaliyar ruwa
Image caption An kuma samu aman wutar dutsi

Mutane sama da dari suka mutu a sakamakon wata mummunar igiyar teku a Indonesiya.

Wata girgizar kasa mai karfin gaske da ta auku a kusa da gabar tekun Sumatra a jiya, ita ta haddasa murdawar mummunar igiyar tekun.

Jami'ai a kasar na kuma ta kokarin daukar matakan shawo kan matsalar aman da dutse ke yi a tsaunin Merapi dake yankin Java ta tsakiya.

Dagacin daya daga cikin kauyukan da bala'in ya shafa, Heri Suprapto, ya ce wasu daga cikin mutanan na can sun rasa yadda za su yi, amma am samu sakonsu ta wayar salula cewa suna nan kalau.