Cin hanci ya karu a Nigeria - in ji Transparency International

Cin hanci da rashawa
Image caption Cin hanci da rashawa

Sabon rahoton kungiyar nan mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, watau Transperancy International ya ce, Najeriya ta samu koma-baya a yaki da cin hanci da rashawa.

A rahotonta na wannan shekarar, kungiyar Transparency International ta ce Nigeria ita ce kasa ta 134 daga cikin 178 a jerin kasashen da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa.

Haka nan ita ma jamhuriyar Niger ta samu karuwar aikace aikacen cin hanci da rashawa, amma duk da haka ita ce kasa ta 123 a jerin kasashen.

Kasar Somalia kamar yadda kungiyar ta ce ita ce inda aka fi fama da cin hanci da rashawa, inda kasar ta zo ta karshe a cikin kasashen 178.

Kasar Denmark ita ta zo ta daya a jerin kasashen, inda ba kasafai aka cika samun matsalar cin hanci da rashawa ba.

Rahoton ya ce, kasar Ghana ta samu cigaba sosai a yaki da cin hanci da rashawan.