A yankewa Tariq Aziz hukuncin kisa

Wata Kotu a Iraqi ta yankewa Tariq Aziz hukunci kisa, bayan ta same shi da laifin murkushe jam'iyyun siyasa yan shi'a a lokacin mulkin marigayi Sadam Hussien.

Tariq Aziz dai a lokacin Mulkin marigayi Sadam Husseini ya yi aiki a matsayin mataimakin firayim minista da kuma ministan harkokin waje.

Tsohon ministan dan shekaru saba'in da duhu yanzu ya dai mika kansa ne jim kadan bayan mamaye kasar ta Iraqi ne da Amurka ta yi a shekarar 2003.

Kuma tun a wancan lokacin ne ya ke tsare, inda tuni ya fuskanci wasu shari'o'in guda biyu. Abinda yasa aka yanke masa hukuncin dauri saboda samunsa da laifin rataye wadansu 'yan kasuwa da ake zargi sun aikata almundahana, da kuma raba Kurdawa da matsugunansu.

Bashi da koshin lafiya

Sai kuma gashi yanzu Kotun kolin kasar ta yankewa Mista Aziz, wanda a halin da ake ciki ba shi da koshin lafiya, hukuncin ratayewa.

An yanke masa hukuncin ne tare da wadansu jam'ian gwamnatin Saddam biyu, wato tsohon ministan harkokin cikin gida kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar, Sadoun Shakir da kuma Sakataren Saddam, Abed Hamoud.

Baki daya an same su ne da laifin murkushe jam'iyyun 'yan shi'a, musamman Jam'iyyar Dawa ta Firayim Minista mai ci Nouri al-Maliki, a shekarun 1980 da 1990.

Dan Mista Aziz, Zaid Tariq Aziz ya shaidawa BBC cewa, wannan hukunci da aka yankewa mahaifinsa ramuwar gayya ce kawai.

Image caption Marigayi Sadam Husseini

Ya ce; "Mahaifina ba shi da laifi domin kuwa kowa ya san ba shi da hannu a irin wadannan al'amuran."

"Shi dan siyasa ne wanda da kafofin yada labarai kawai ya yi hulda ba abubuwan da suka shafi tsaro ba."

" Hanya kawai Gwamnatin Iraqi ke nema ta kashe shi kamar yadda ta ke neman hanyar kashe jami'an tsohuwar gwamnati, shi ya sa ta zarge shi da wadannan laifuffuka."

Ko da yake Tariq Aziz ya kasance fitacciyar muryar gwamnatin Saddam Hussain, musamman ga kasashen ketare, a matsayinsa na mataimakin firayim minista da kuma ministan harkokin waje, ba ya cikin wadanda ake dauka masu karfin fada a ji a jami'iyyar Ba'ath.

Shi dai Mista Aziz Kirista ne, yayin da dukkan kusoshin jam'iyyar ta Ba'ath dangin Saddam ne 'yan Sunni.