Wasu nau'in dabbobi na neman bacewa daga doran kasa

Wata Giwa a cikin daji
Image caption Wani rahoto da aka fitar akan halinda dabbobi ke ciki a duniya yayi nuni da cewar akwai wasu nau'in dabbobi dake neman bacewa a doran kasa yanzu haka

Wani rahoto da kungiyar kasa da kasa dake kula da yanayi ta wallafa akan halin da dabbobi a fadin duniya ke ciki, ya ce kimanin nau'in dabbobi hamsin ne ke neman bacewa a doron kasa a kowace shekara.

Rahoton yayi nuni da cewa adadin dabbobin dake rayuwa a cikin ruwa na matukar raguwa fiye da sauran dabbobin dake rayuwa a doron kasa, inda rahoton ya ce da ba don kokarin kungiyar kula da yanayin ba, da adadin ya zarta haka.

An dai fitar da wannan rahoton ne a kwanakin karshe na taron kasa da kasa kan yanayi a kasar Japan inda mahalarta taron ke tattauna matsalar bacewar dabbobi a doron kasa.

Yayin da ya rage kwanaki uku a kammala taron, kawunan gwamnatoci sun rarrabu dangane da muhimman batutuwan da suka hada da ko nawa ne kasashen yammacin duniya zasu rika bayarwa domin taimakawa wajen adana kula da dabbobin.