An nuna wasu daga cikin makaman da aka cafke a Lagos

Wani dan bindiga a Nijeriya
Image caption Wani dan bindiga a Nijeriya

Yau ne hukumomin tsaro a Nijeriya suka nuna wasu daga cikin makaman da suka kama a cikin wasu manyan akwatuna ko Kwantainoni.

Makaman dai sun hada da roka da gurneti da kuma alburusai masu yawan gaske.

Jiya ne jami'an tsaro na farin kaya na SSS suka kama kwantainonin 13 dauke da makaman a tashar jiragen ruwa ta Apapa dake Lagos, bayan wani jirgin ruwa ya sauke su.

Hukumar ta SSS dai ta ce an shigo da makaman ne a boye inda aka fake da cewa kayan gini ne.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro a Nijeriyar ba su bayar da wani karin bayani ba akan inda jirgin ya fito ko inda za shi.