Osama Bin Laden ya gargadi Faransa

Osama Bin Laden
Image caption al-Qaeda ta dade tana barazana ga kadarorin kasashen yamma a Afrika

Jagoran kungiyar al-Qaeda Osama Bin Laden, ya alakanta sace ma'aikatan Faransa 5 da aka yi a Nijar, da yadda Faransan ke muzgunawa musulmai a kasar ta.

A wani sako da ya aike ta fefen rediyo, shugaban na al-Qaeda ya ce kamen, martani ne ga "rashin adalcin da kasar ke nunawa musulmai".

Sakon yace haramcin da Faransa ta sanya kan amfani da Burqa alamace da ke nuna "irin zaluncin 'yan mulkin mallaka".

Mai maganar ya kuma nemi Faransa ta janye sojojinta daga kasar Afghanistan.

Bin Laden, wanda ake zargi da shirya hare-haren 11 ga watan Satumba, shi ne mutumin da Amurka ta fi nema ruwa a jallo.

Kuma a yayinda wasu ke ganin tuni aka kashe shi, wasu na ganin yana nan yana rayuwa a yankunan Pakistan da Afghanistan.

'A baiwa mata 'yanci'

Kungiyar al-Qaeda ta kama 'yan kasar Faransa biyar da wasu jama'a biyu daban, a wani wurin hakar ma'adanan Uraniyom a watan da ya gabata.

Kuma yanzu ana hasashen cewa ana tsare da su ne a arewa maso yammacin kasar Mali.

Hasashen da kuma jami'an kasashen na Mali da Nijar suka tabbatar.

Mai maganar wacce aka watsa a gidan talabijin na al-Jazeera, ya bayyana kamen Faransawan da cewa martani ne ga yadda kasar ke muzgunawa kasashen musulmi.

Mai maganar ya ce idan har Faransa na son kare kanta, to wajibi ne ya fice daga tawagar Amurka da ke yakar Afghanistan.