Ba za'a sami nasara ba a Afghanistan-in ji Gorbachev

Mr. Mikhail Gorbachev
Image caption Tsohon shugaban tarayyar sobiyat Mikhail Gorbachev yayi gargadin cewar ba za'a taba samun nasara ba a yakin Afghanistan

Tsohon shugaban kasar Rasha Mikhail Gorbachev ya gargadi kungiyar kawance ta NATO cewa samun nasarar soji a Afghanistan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.

Mr Gorbachev, wanda ya janye dakarun Rasha a Afghanistan fiye da shekaru ashirin da suka gabata, ya shaidawa BBC cewa abin da za'a iya yi shine a taimakawa kasar ta sake farfadowa.

Ya kuma jinjinawa shugaban Amurka Barrack Obama na shawarar fara janye dakarun Amurkan a Afghanistan, sai dai ya soki matakin Amurkan na kasancewa a yankin na tsawon shekaru da dama.

Yace samun nasara ba zai taba yiwuwa ba a Afghanistan, shugaba Obama yayi dai dai na shawarar janye dakarun kasar, kowace irin wahala ce kuwa za'a fuskanta.