Majalisar wakilan Nijeriya ta amince da gyaran kundin tsarin mulki

Zauren majalisar dokokin Nijeriya
Image caption Zauren majalisar dokokin Nijeriya

A zaman da ta yi dazu majalisar wakilan Najeriya ta amince da gyaran da aka yiwa wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar da suka shafi gudanar da zabe.

Hukumar zabe ta kasa, wato INEC ce ta nemi ayi wannan gyara domin ba ta karin lokacin da tace, tana bukata wajem shirya zabe mai inganci.

Nan da mako mai zuwa ne dai ake sa ran mikawa majalissun dokokin jihohin Najeriyar 36 wannan sabon kundin tsarin mulki domin neman amincewarsu.