Ministan wajen Kenya ya ajiye aiki

Ministan kula da harkokin wajen Kenya, Moses Wetangula , ya sauka daga mukaminsa, yayin da ake ci gaba da takaddama a kasar game da badakalar sayen wasu gidaje na ofishin jakadancin kasar a Japan.

A ranar Talata majalisar dokokin kasar ta Kenya ta tabka muhawara kan wani rahotan da ya bada shawarar cire ministan daga kan mukaminsa kan wannan lamarin.

Rahotan ya ce Kenya ta yi asarar dala miliyan sha hudu, wajen sayen wani sabon ofishin jakadancin kasar a Japan, haka nan kuma ta yi asarar makudan kudade a ofisoshin jakadancinta dake Najeriya, da Pakistan da kuma Belgium.

Mr Wetangulu dai ya musanta aikata wani laifi.