An sabunta: 27 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 13:28 GMT

Kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin Nijar

Salou Jibou

A watan Fabreru za a gudanar da zabe domin maida mulki ga farar hula

A jamhuriyar Nijar, ranar Lahadi ne za a gudanar da kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a ci gaba da shirye-shiryen da ake na maida kasar kan tafarkin dimokradiyya.

Shi dai wannan sabon kudin ya tanadi tsarin mulki ne mai ruwa biyu, inda shugaban kasa yake raba iko da Pira Minista.

Shin ko wannan tasrin mulki ya dace da yadda al'amura suke a jamhuriyar ta Nijar?

Kuma shin jama'a sun fahimci tanade-tanaden tsarin mulkin?

Wadannan na daga cikin tambayoyin da za mu yi kokarin amsawa tare da ku masu sauraro a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako.

To domin shiga cikin shirin sai ku aiko mana da takaitattun ra'ayoyinku ta adreshinmu na email, wato hausa@bbc.co.uk, ko kuma ta dandalin mu na muhawara, BBCHausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na internet, bbchausa.com

Ko kuma ta hanyar cike wannan gurbin:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.