Majalisa ta amince da gyaran kundi

A zaman da ta yi dazu majalisar dattawan Najeriya majalisar ta amince da wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin kasar da suka shafi zabe.

Hukumar zabe ta kasa ce dai ta nemi a yi wasu daga cikin gyare-gyaren domin ba ta karin lokacin kintsawa zaben na badi.

Bayan majalisar wakilai ta nuna amincewarta , za a mika batun ga majalisun dokoki na jihohi domin su ma su tafka muhawara kansa.

A ciki da wajen Najeriya dai an zura ido ne domin ganin zaben na badi ya fita zakka.