Al-Shabab ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 2

Mayakan kungiyar al-Shbab
Image caption Kungiyar al-Ashabab na iko da mafiya yankunan kasar

A Somalia, kungiyar masu kishin Islama ta al-Shabab ta aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama'a kan wasu mata biyu, wadand ake zargi da leken asiri.

Yankuna da dama na Somaliar dai na karkashin ikon Kungiyar ta al-Shabaab mai ra'ayin gani kashe nin Islama.

An harbe matan ne, wadanda da kadan suka haura shekaru ashirin a duniya, ranar Laraba a garin Belet Weyn. An kuma ba da rahoton cewa an harbe su ne a bainar dimbin jama'a.

Kwamandan mayakan sa kai na al-Shabab a yankin yace an samu matan ne da laifin aikata leken asiri ga wadanda ya kira makiya addinin Musulunci.

Ita dai kungiyar Al Shabab tana yaki ne da gwamnatin kasar mai rauni wadda dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar afirka ke ba kariya, kuma kwanan nan banagarorin biyu suka fafata kusa da garin na Belet Weyne.

Tun shekarar 1991 ne dai kasar ta Somaliya ke cikin dimuwa, mutane da dama kuma na mata kallon kasar da ta fi ko wacce rashin zaman lafiya a duniya.