Ambaliyar ruwa ta shafi dubban mutane a Ghana

Taswirar Ghana
Image caption Mutane suna neman taimako

Hukumomi a arewacin Ghana sun ce suna iya kokarinsu wajen taimaka wa dubban mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, ambaliyar da ake cewa ita ce mafi muni a tarihin kasar.

Shugaban karamar hukumar Gonja, Salisu Bewuribe, ya shaida wa BBC cewa kayan agajin da suka tanadar wa mutanen da ambaliyar ta shafa, ba su wadatar ba.

Ya yi kira ga kungiyoyin agaji su gaggauta cika alkawuran da suka dauka na taimakawa.

A jiya, wani wakilin BBC ya tarar da da mutane da dama na jiran a kai masu dauki.

Mutane akalla dubu ashirin da biyar ne ambaliyar ruwan ta shafa, bayan da aka kwashe makonni biyu ana tabka ruwan sama.