Kayan agaji sun fara isa Indonesia

Tsunami
Image caption Jirgin agaji na sauka a tsibirin Mentawei da girgizar kasa ta daidai ta

Jami'ai a Indonesia sun ce a karshe dai kayan agaji sun fara kaiwa ga jerin tsibiran Mentawei na kasar Indonesia, wadanda igiyar ruwa ta tsunami ta yiwa ta'adin gaske.

Ana sa ran Shugaban Indonesia'r, Susilo Bambang Yudhoyono, zai ziyarci yankin a ranar Alhamis.

Mutane fiye da dari uku ne suka rasa rayukansu a sakamakon wannan masifa da ta afkawa yankin yayin da har yanzu ba'a san inda wasu daruruwan mutane suke ba.

Jami'ai a hukumar ba da agajin gaggawa ta Indonesia sun ce yayinda ake kara fahimtar irin ta'adin da bala'in girgizar kasa ya yi a Tsibirin Mentawai, ayyukan ba da agaji ka iya daukar mako daya ko ma fiye.

Rashin kyawun yanayi na cikin manyan kalubalen da kungiyoyin masu ba da agaji ke fuskanta.

Ana fuskantar matsala

Shugaban kungiyar ba da gaji ta Red Cross a Yammacin Sumatra, Hidayatul Irham, ya shaidawa BBC cewa ma'aikatan agaji na fuskantar matsalar ababen hawa da kuma sadarwa.

Ya ce har yanzu muna kokarin mu samu ababen hawan da zamu yi amfani da su mu da sauran kungiyoyi.

"Yanayi ya sauya--da safe akwai kyakkyawan yanayi amma rana na yi sai aka fara ruwa ba zato ba tsammani."

'Har yanzu babu duriyarsu'

Wasu daga cikin ma'aikatan mu sun samu damar isa wuraren da abin ya shafa amma har yanzu babu duriyarsu. To amma dai kayan agajin sun fara isa yankin na Mentawai.

Wani jirgin ruwa dauke da tufafi da barguna da abinci da magunguna ya isa Tsibirin Arewacin Pagai.

Ana sa ran wani ayari da ke wa Shugaban kasar Susilo Bambang Yudhyono rakiya zai kai karin kayan agaji nan gaba a yau.