Daruruwan jama'a sun bata a Indonesia

Kasar Indonesia
Image caption Jami'an hukumar kula da yanayin sun dora alhakin bala'oin da lalacewar na'urorin hango aukuwar ire iren wadannan bala'oi

Har yanzu ba a ji duriyar daruruwan mutane ba kwanaki da dama bayan da mummunar girgizar kasa tare da igiyar ruwa ta Tsunami ta afkawa wasu yankunan Indonesia.

A kalla mutane 343 ne suka rasa rayukansu a tsibirin Mentawai, yayinda ba a ji duriyar kimanin 400 ba.

Jami'ai a kasar sun ce akwai yiwuwar guguwa da girgizar kasar ta yi awangaba da su.

A kalla kauyuka goma sha uku ne dake tsibirin Mentawai, wannan bala'in ya yi matukar shafa, inda aka tabbatar da mutuwar fiye da mutane dari uku, yayin da kuma wasu mutane dari hudu suka bace.

Jami'an hukumar kula da yanayin kasar dai sun bayyana cewar na'urorin gargadin abkuwar girgizar kasar da kuma ambaliyar ruwa da aka sanya, bayan ambaliyar ruwa ta tsunami shekaru shida da suka gabata, sune basa aiki kamar yadda ya kamata.

A saboda haka jami'an hukumar sun dora alhakin jerin bala'oin da suka fadawa kasar sanadiyyar rashin lalacewar na'urorin