Ana samun rudani game da makaman da aka kama a Najeriya

Irin makaman da aka kama a Najeriya
Image caption Makaman sun hada da roka da gurneti da kuma albarusai

Hukumomi a Isra'ila sun ce makaman da aka kama a Najeriya sun fito ne daga kasar Iran akan hanyarsu ta zuwa Zirin Gaza, sai dai jami'an Hamas sun yi watsi da kalaman na su.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ambato jami'an sojin Isra'ila suna zargin Iran, amma ba su bada wata hujja ba.

Sai dai kalaman na su sun saba wa na jami'an Customs na Najeriya, wadanda suka ce an kawo makaman ne Najeriya daga India.

Shi ma dai Ismail Radwan, jagoran Hamas a Gaza, ya musanta cewa yankin Zirin Gaza aka nufa da makaman.

Kakakin hukumar Customs, Mista Wale Adeniyi ya shaida wa BBC cewa, jirgin mai suna Everest ya taso ne daga kasar India, inda ya sauke abubuwan da yake dauke da su a tashar jiragen ruwa ta Legas a watan Yulin da ya wuce.

Mallaka

A nasu bangaren, kamfanin jirgin mai suna CMA-CGM, wanda ke da hedikwata a Faransa ya fitar da wata sanarwa inda ya ce, kwantenonin na wani kamfani ne.

Kakakin kamfanin ya shaida wa BBC cewa, a matsayinsu na masu jigilar kayayyaki, sun loda duk abubuwan da jirgin ke dauke dasu ne don kai su wajen da ya kamata, kuma babu abinda suka taba a cikin kayan har lokacin da jirgin ya isa Najeriya.

Image caption Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Janar Azazi lokacin da ya ziyarci tashan ruwan ta Legas

Sai dai ya ce, sun samu bayani daga jami'an tsaron Najeriya kan kwantenonin, kuma za su bada cikakken hadin kai wajen gano mutumin da ke dasu.

Tabarbarewar tsaro

Koda BBC ta tuntubi minista a ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Hajiya Salamatu Suleiman ta ce, ba ta kasar don haka ba za ta iya cewa komai akan batun ba.

Shi ma wani jami'in ofishin jakadancin Iran da ke Najeriya ya shaida BBC cewa sai a ranar Juma'a ne za su yiwa manema labarai bayani kan batun.

A ranar talatar data gabata ne dai, hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta ce ta cafke kwantena goma sha uku a jihar Lagos, wadanda kuma bayan ta bude hudu daga ciki ta samu Makamai da suka hada da roka da gurneti da kuma albarusai.

Wannan lamari dai ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da nuna shakku kan yanayin tsaro a kasar.

Ga kuma harin bom din da aka kai a ranar da kasar ke bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai, da kuma hare-haren sari ka noke da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram na kaiwa a wasu jihohin kasar.