Shugaba Obama ya kare irin matakan da yake dauka

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewar yana bukatar karin lokaci kafin a ga dukkanin matakan da yai alkawarin gudanarwa

A lokacin daya bayyana a shirin gidan wani talabijin na ban dariya, Shugaban Amurka Barack Obama ya nemi kare irin matakan da yake dauka a kasar.

Kalaman shugaban na zuwa ne kwanaki kadan kafin a gudanar da zaben rabin wa'adin mulki, inda ake kyautata zaton jam'iyarsa ba zata tabuka wani abin azo a gani ba.

Mr. Obama ya shaidawa mai gabatar da shirin Jon Stewart cewa, sauye sauyen da yayi alkawarin gudanarwa a kasar ba abubuwa bane da za su yiwu cikin watanni goma sha takwas.

Shugaban ya kuma musanta cewa gwamnatinsa bata sassauci duk kuwa da ikirarin da jam'iyarsa tayi a lokacin yakin neman zabe cewa zata rika cizawa tana hurawa, inda ya ce ko kadan bai yarda cewa sabon shirinsa na kiwon lafiya yana da tsauri ba.