An kama dakunan sarrafa miyagun kwayoyi a Afghanistan

Jami'an tsaron Amurka
Image caption Afghanistan ta yi kaurin suna wajen mu'amilla da miyagun kwayoyi

Jami'an yaki da fataucin miyagun kwayoyi na Amurka da Rasha, sun kama wasu dakuna hudu da ake sarrafa miyagun kwayoyin a Afghanistan.

Ana dai daukar wannan samame da muhimmanci ganin cewa shi ne irinsa na farko da Amurka da Rasha suka hada gwiwa don kaiwa.

Jami'an sun kama fiye da tan daya na hodar Heroin, wadda darajarta ta zarta dala miliyan 50, da kuma ganyen opium mai yawa, alardin Nangarhar dake kusa da iyaka da Pakistan.

Hukumomin yaki da miyagun kwayoyi a kasar ta Rasha sun ce, dabarun da aka yi amfani da su wajen kai samamen ne, suka basu damar samun nasara.

An yi amfani da jiragen yaki

Shugaban hukumar daki yaki da miyagun kwayoyi ta Rasha, Viktor Ivanov ya ce, an yi amfani da jirage masu saukar ungulu, wajen kai farmaki ta sama:

Mun yi amfani da helikoftoci har guda 9, masu kai hari 3 da kuma masu tallafawa 6. Mun gaano tare da lalata wurare 4 inda ake harhada miyagun kwayoyi na heroin da morphine.

Wakilin BBC a Mosko ya ce samamen, wata alama ce ta irin karin hadin kan da ake samu tsakanin Amurka da Rasha dangane da batun Afghanistan.

A zahiri dai, dakunan yin hodar ibilis din guda uku ne, da kuma wani dakin da ake yin koken samfurin morphine.

Rasha ta bayyana farmakin da cewa, shi ne gagarumin farmaki kan dakunan sarrafa miyagun kwayoyi, wadanda ake kaiwa kasashen tsakiyar Asia.

Ta ce, samamen ya yi maganin amfani da ake yi da miyagun kwayoyi wajen gudanar da manyan laifuka, da ta'addanci, da kuma samar da masu tsattsauran ra'ayi a kasashen yankin.

Karsar ta Rasha ta kara da cewa, farmakin ya samu nasara ne sakamakon wasu bayanan sirri da ta samu daga Amurka.

Wannan shi ne karo na farko da kasashen biyu, suka hada gwiwa don kaddamar da farmaki, kuma hakan wata alama ce dake nuna irin hannnun da kasar Rasha ke da shi a cikin al'amuran Afghanistan.