Amurka ta shawarci Angola akan fyade

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Amurka ta bukaci kasar Angola ta gudanar da bincike kan wasu mata da ake zargin anyi wa fyade

Amurka tayi kira ga kasar Angola data binciki zargin aikata fyade da aka yiwa wasu mata wadanda aka korosu daga jamhuriyar Demukradiyyar Congo

Amurkan tace wajibi ne ga kasashen su kare 'yancin mata da kananan yara.

Kakakin gwamnatin Amurka Philip Crowley, ya ce akwai bukatar kasashen biyu su yi amfani da matakan da a kulla na karfafa dangantaka tsakaninsu wajen magance matsalar yin kaura akan iyakokin kasashen.

A shekarar 2004 ne dai kasar Angola ta kaddamar da wani shiri da yayi sanadiyar korar fiye da bakin haure dubu hudu daga wuraren hakar ma'adinai dake kasar wadanda akasarinsu 'yan kasar Congo ne.

Hakan ya sa itama kasar Congo ta kori wasu bakin haure 'yan kasar Angola dake kasar.