Kasashen China da Japan zasu daidaita tsakaninsu

Shugabannin kasashen China da Japan
Image caption Kasashen China da Japan na wani yunkuri na daidaita tsakaninsu

Ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Japan sun gana a Hanoi a wani yunkuri da zai taimaka wajen sassauta ce-ce ku-ce tsakanin kasashen biyu.

An ammbato Ministan harkokin wajen kasar Japan Seiji Maehara, na cewa shi da takwararsa na kasar Sin, Yang Jiechi, sun amince su inganta dangantaka tsakanin kasashensu.

A watan daya gabata ne dai danganta ta fuskar diplomasiya tsakanin kasashen biyu tayi tsami dangane da tsibirin nan dake gabashin tekun kasar Sin da