A Najeriya wasu sun ce Shugabanci sai arewa

PDP
Image caption PDP

A Najeriya, har yanzu wasu kungiyoyin matasa na bayyana matsayinsu game da batun shugabancin kasar ya kasance da ga arewa, karkashin inuwar jam'iyar PDP.

To sai dai kuma duk da cewa akwai mutane da dama daga arewar dake son tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jamiyyar ta PDP, har yanzu kungiyoyin basu bayyana in da su ka karkata ba.

Su dai kungiyoyin na kira ne kan a tsayar da dan arewa ko ma waye a cikin 'yan takarar domin zaben shugabancin kasar da za'a yi a badi

Hatta wadanda ba 'yan jamiyyar PDP ba ma na tofa albarkacin bakinsu game da tsarin mulkin karba- karba da jamiyyar PDP ta fito da shi.

Jam'iyar PDP ta bullo da wannan tsari ne domin samun maslaha a tsakanin bangarori daban-daban a kasar, wanda kuma wannan wani batu ne na ta na cikin gida.