A Najeriya Jihohin Ribas da Abiya na takun saka

A Najeriya, wata takaddama ta kunno kai tsakanin jihohin Ribas da Abia, da ke yankin Kudu maso Kudanci da kuma Gabashin Kasar.

Takaddamar dai ta taso ne sakamakon wani furuci da Gwamanar Jihar Ribas Mista Chubuike Rotimi Ameachi, ya yi in da ya ke cewa Jihar sa ta kashe Kudade masu yawa wajen kara tsaurara matakan tsaro a Jihar Abiya.

Wannan batu bai yi wa hukumomin Jihar Abiya wadda ke makwabtaka da Jihar Ribas din dadi ba, lamarin da har ya kai jihohin biyu nunawa juna yatsa.

Hukumomin Abiya sun ba da martani cewa ya kamata Gwamnatin Jihar Ribas din ta mayar da hankali akan Jihar ta, ta daina yi musu katsalandan.

Sun kuma kara da cewa a iya saninsu ba bu wata Jiha a Najeriya da ta ke da Jami'an tsaro na kanta, wanda har wani Gwamna zai bugi kirji ya ce sakamakon sa hannunsa ne aka samu zaman lafiya a Jihar Abiya.

Gwamnatin Jihar Ribas dai ta bayyana cewa ba za ta kula da abin da hukumomin Jihar Abiya ke cewa ba, tun da sun riga sun yi taimakon, kuma kowa ya san cewa Gwamnatin Ribas din ta taka mahimmiyar rawa wajen kawar da 'yan zauna gari banza a garin Aba da ke Jihar Abiyan.

Jihar Abiya a 'yan kwanakin nan ta yi kaurin suna wajen fashi da makami da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Lamarin kuma da ya sa hukumar tsaro su ka tsaurara matakin da ya kai ga kame fiye da mutane dari a watan da muke ciki, wadanda ake zargi da aikata fashi da makami da kuma satar mutane domin neman fansa a jihar ta Abiya.