Nijeriya ta yaba da shirin mayar da Nijar kan turbar Demokradiyya

Tutar Jumhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jumhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar yayin da ya rage kwana biyu a gudanar da zaben raba gardama a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, jakadan Najeriya a Nijar din, Ambasada Bature Lawal, ya nuna gamsuwarsa da shirin hukumomin mulkin sojin kasar ta Nijar, na mayar da kasar kan turbar demokaradiya.

A wata hira da manema labarai yau da safe a birnin Yamai, jakadan na Nijeriya yana ganin shirya zabubuka na gari da kowa ya amince da su a nijar din da nijeriya, shi ne zai tabbatar da demokaradiya da ci gaban kasashen biyu.

'Yan Nijar kusan miliyan shidda da rabi ne dai za su kada kuriar rabagardamar a kan sabon tsarin mulkin, kuma galibin jam'iyyun siyasar kasar sun yi kira ga magoya bayansu da su amince da kundin.