Shugaba Obama ya ce Al Qaeda ce ta turo sako

Shugaba Barack Obama ya bayyana cewa sakonnin da aka samu a filin jirgin saman Dubai, na kunshe ne da abubuwan da ka iya haddasa wuta.

An aiko da sakonnin ne daga Yemen da zummar kai su wadanusu wuraren bautar yahudawa a Chicago.

Mista Obama dai ya bayyana cewa wannan wata barazana ce ta harin ta'addanci, in da ya bayyana cewa duka sakonni biyun sun samo asali ne daga Yemen, kuma sun fito ne daga tushe guda.

Mista Obama dai ya bayyana cewa sakonnin na da nasaba da kungiyar Al- Qaeda.

Mai baiwa shugaba Obama shawara akan harkar da ta shafi yaki da ta'addanci John Brennan ya bayyana cewa a yanzu haka, Yemen ce za ta kasance wurin da binciken su zai fi bada karfi.

Jami'ai da ga fadar White House dai sun bayyana cewa sun jiyo kishin kishin din sakonnin ne da ga wurin Saudi Arabia.