Ana cikin shirin ko-ta-kwana a Amurka da Burtaniya

Jirgin da ake zargin yana dauke da sinadarin bom
Image caption Jirgin kamfanin UPS kenan da ake zargin yana dauke da sinadarin bom

Jami'an Amurka sun ce halin ko-ta-kwanan da ake ciki yanzu haka a wasu filayen tashin jiragen sama da ke Amurka da Burtaniya sun biyo bayan wasu kunshin kaya ne da ake zargin bama-bamai ne a wani jirgin kaya da ya taso daga Yemen zuwa Amurka.

Kwamishinan 'yan sandan New York Ray Kelly, ya ce akwai damuwa game da wasu kunshin kaya da suka taso daga Yemen a jiragen kamfanonin UPS da Fedex zuwa filayen jiragen sama da dama da ke Amurka.

Babu dai wani abu da aka gani a kunshin kayan da aka bude.

Sai dai hukumomi sun ce za a tsaurara matakan tsaro wadanda za su hada da karin bincike kan jiragen daukar kaya.

A Burtaniya kuma 'yan sanda sun ce jirage sun fara tashi daga fiin jiragen sama na East Midlands wanda aka rufe da farko bayanda aka cire wani kunshin kayan da aka zargin bom ne daga wani jirgin da ya taso daga Yemen da nufin isa garin Chicago a Amurka.

An gudanar da bincike kan jiragen daukar kaya a filayen saukar jiragen sama na New Jersey da Philadelphia a Amurka.

An dauke jiragen zuwa wajen gari a Amurka domin a bincikesu.

Tun da farko wani rahoto da ba a tabbatar ba da gidan talabijin na CNN ya fitar, ya ce an samu sinadarin bom a jirgin da ya taso daga Yemen zuwa Chicago a Amurka, bayanda aka tsaida shi a Burtaniya.