Ana cigaba da gudanar da zaben shugaban kasa a Ivory Coast

ivory coast
Image caption Taswirar Ivory Coast

A Ivory Coast dimbin jama'a sun fito domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar, wanda shine na farko a cikin shekaru goma.

Ana sa ran zaben zai kawo karshen rikicin da kasar ta yi fama da shi.

A duk tsawon yini an sami dogayen layuka a birnin Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar, har ma ta kai rumfunan zabe da dama sun rasa na yi.

'Yan takara goma sha hudu ne ke fafatawa a zaben, amma wadanda ke kan gaba sune shugaba mai ci a yanzu, Laurent Gbagbo, da tsohon shugaban kasar Henri Konan Bedie, sannan da tsohon Praminista Alassane Ouattara.

Masu kada kuri'a a kasar kimanin su miliyan shida na da 'yancin zabar duk wanda su ke so daga cikin 'yan takara goma sha hudu da suka tsaya, wanda a cikinsu a karo na farko har da mace da kuma wani daga arewa, wato yankin da aka ware a lokacin rikicin shekarar 2002.

A baya an dakatar da babban dan takara daga arewan, kuma tsohon mai yiwa asusun bada lamuni na duniya sharhi akan tattalin Arziki Alasan Watara daga tsayawa zabe, duk da cewa yana da ga cikin wadanda suka samu karbuwa.

Manyan abokan adawarsa sun hada da shugaban kasar mai ci Lauren Bakbo da kuma tsohon shugaban kasar Henri Konan Bedie, wanda aka hantsilar da gwamnatinsa a yayin wani juyin mulki a shekarar 1999.

'Yan takarar dai na fuskantar kalubale iri daya, wato na farfado da tattalin arzikin kasar da samarwa matasan aiyukan yi da kuma dakatar da tashe tashen hankula.

Sai dai kuma mafi yawan masu kada kuri'ar na fargabar abinda ka iya biyo baya, idan aka tabbatar da sakamakon zaben, musamman ma idan su ka yi la'akari da yakin basasar da ya barke a kasar a shekarar 2002.

Alamu dai na nuni da cewa akwai yiwuwar tazarar kuri'un ta kasance gab da gab, wanda hakan ka iya sawa a yi zagaye na biyu.