Zaben raba gardama a Nijar bai kawo kallo ba

Nijar
Image caption Tutar Nijar

A jamhuriyar Nijar yau ne 'yan kasar suka kada kuri'ar raba gardama dangane da wani sabon kundin tsarin mulki da Majalisar Mulkin Soja ta CSRD ta gabatar musu.

Sabon kundin tsarin mulkin ya tanadi wasu sauye-sauye da suka hada da kayyade wa'adin mulki ga zababben shugaban kasa zuwa shekaru biyar sau biyu kacal, yayin da 'yan majalisar dokoki za su iya tsige kakakin majalisar.

Fiye da mutane miliyan shida ne ya kamata a ce sun kada kuri'unsu, domin amincewa ko kuma kin amincewa da sabon kundin tsarin mulkin, wanda zai share fagen sauran zabubukan da za a gudanar a Nijar din a nan gaba.

Rahotanni sun ce masu zabe dayawa basu fita ba domin jefa kuri'ar.

Nan da sa'o'i 72 ake sa ran samun sakamakon kuri'ar raba gardamar.