Al'ummar Nijar na kada kuri'ar raba gardama

A jamhuriyar Nijar yau ne 'yan kasar suke kada kuri'ar raba gardama dangane da wani sabon kundin tsarin mulki da Majalisar Mulkin Soja ta CSRD ta gabatar musu.

Sabon kundin tsarin mulkin ya tanadi wasu sauye-sauye da suka hada da kayyade wa'adin mulki ga zababbaben shugaban kasa zuwa shekaru biyar sau biyu kacal, yayin da 'yan majalisar dokoki za su iya tsige kakakin majalisar.

Fiye da mutane miliyan shida ne dai ake tsamanin za su fito domin kada kuri'a a yau.

Sai dai wata matsala ita ce, har yanzu, wasu 'yan kasar basu san bayanan da sabon kundin ya kunsa ba.