Kotun Sojin Amurka ta yankewa Umar Khadr hukunci

Image caption Umar Khadr

Wata kotun soji da ke Amurka ta yankewa Omar Khadr wanda ke da mafi karancin shekaru a cikin wadanda ake tsare da su a gidan kason Guantanamo Bay, hukuncin daurin shekaru arba'in a gidan yari.

Sai dai kuma rokon neman afuwa da ya gabatar ya sanya an rage hukuncin zuwa shekaru takwas.

Mista Khadr dai shine mutum na farko tun bayan yakin duniya na biyu da wata kotun sojin Amurka ta yanke wa hukunci akan aikata laifuka a lokacin da yake da karanchin shekaru.

A makon da ya gabata, Omar Khadr wanda yanzu haka ke da shekaru ashirin da hudu, ya amsa laifuka biyar din da ake zarginsa da aikatawa, ciki har da jefa gurnetin da yayi ajalin wani sojin Amurka dake aiki a Afghanistan.

A wancan lokacin ya na da shekaru goma sha biyar.

Matar sojin Amurkan da Omar Khadr ya janyo ajalinsa, a yayin da ta ji hukuncin da kotu ta zartar, ta bayyana jin dadinta da haka.

To sai dai kuma Lawyan Mr. Khadr din ya bayyana cewa sam ba a yi adalci a shari'ar ba, domin dai a lokacin da abin ya faru, ya na yaro, kuma ya kasance irin yaran da ake tursasawa su yi fada ne.