Wata kungiya ta kalubalanci Ban Ki Moon

Kungiyar Human Rights Watch wadda ke birnin New York na Amurka, wadda ke kare hakkokin bil adama ta kalubalanci Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya game da kin tabo batutuwan da suka shafi hakkokin bil adama a yayin ganawarsu da shugaban kasar Sin.

Kungiyar Human Rights Watch din ta bayyana takaicinta da kin fitowa fili da Ban ki Moon ya yi wajen bayyana damuwar da ake da ita game da tsare mutumin nan da ya ciyo kyautar yabo a bangaren zaman lafiya a duniya wato Liu Xiaobo.

Mai magana da yawun Mista Ban din dai ya tabbatar da cewa sam basu tattauna batun daurin da ake wa mutumin da Shugaba hu Jintao ba, a yayin wata ganawa da suka yi a jiya litinin.

Kungiyar Human Rights Watch din dai ta bayyana wannan batun a matsayin wani abu mai ban mamaki.

Kungiyar ta ce ya sace gwuiwar masu fafutuka na kasar Sin ta hanyar kin taso da batun daurin da ake yi wa Liu Xiabo a yayin ziyarar da ya kai kasar.

Sai dai an tabo wadansu batutuwa da dama, ciki har da yin kira ga Sin da ta tallafa wajen magance matsalolin da ke faruwa a nahiyar Afirka kamar rikicin Somalia da na Sudan.

Tuni dai masu fafutukar kare hakkokin bil adama suka kalubalanci magatakardar , game da taka tsantsan din da ya ke yi wajen tabo batun daurin da ake yiwa Liu Xiaobo a lokacin da aka bashi kyautar yabo.

A lokacin Mista Ban din dai ya yi wadansu 'yan jawabai ne a fakaice amma sam bai nemi da a sake shi ba.

Shi dai Mista Ban ya kare kan sa ne inda ya bayyana cewa diplomasiyyarsa ba mai zafi bace.

To sai dai masu sharhi akan al'amura sun fassara hakan ne da cewa ya na neman goyon bayan Sin domin yin wa'adi na biyu akan kujerar da ya ke kai.

To sai dai Kungiyar Human Rights Watch din ta bayyana cewa idan har wannan shine hangen Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar, to ta na me tunatar da shi cewa ci gaba da kasancewarsa akan mulki zai dogara ne akan irin kwarin gwuiwar da ya ke bayarwa akan hakkokin bil adama.