A Najeriya, ana tofa ta baka kan Gwamnan Ogun

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, matakin da wasu gwamnonin kasar suka dauka na nada Gwamnan Jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel a matsayin sabon shugaban kungiyar Gwamnoni domin ya maye gurbin Gwamna Bukola Saraki na Jihar Kwara, na ci gaba da haddasa cece-kuce.

Masu nazari akan al'amuran yau da kullum a kasar sun bayyana cewa wannan alama ce ta raunin a tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

A karshen makon jiya ne dai gwamnonin suka ba da sanarwar daukar matakin nada gwamnan Jihar Ogun din a matsayin shugaban su.

Sai dai kuma wasu daga cikin Gwamnonin, musamman Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, sun ce ba da yawunsu aka yi hakan ba.

Masana dai sun bayyana cewa wannan rarrabuwar kan da aka samu a tsakanin Gwamnonin wani mataki ne na siyasa, in da kowanne bangare ke kokarin ganin cewa su ne su ka yi nasara a zaben shugabancin kasar da za'a yi a badi.