Akwai yiwuwar samun karancin abinci a Najeriya

A Najeriya, wani rahoto da kungiyar bayar da gargadi da wuri kan karancin abinci ta fitar ya nuna cewar bala'in ambaliyar ruwan da aka samu tsakanin watanin Yuli da Octoba na bana zai iya haifar da matsalar karancin abinci a wasu sassan kasar.

Jihohin da ake gani abin zai shafa sun hada da Sakkwato, Kebbi da kuma Jigawa dake Arewacin Najeriya.

Rahoton ya ce, sakamakon wani binciken da aka gudanar bayan anyi girbi na bayyana cewa ambaliyar ruwan ta haddasa raguwar yawan abincin da aka girba, tare da lalata wanda aka adana.

Bugu da kari, wannan ya rufe kofofin samun kudaden shiga ga dubban iyalai dake zaune a kusa da kogunan da suka yi ambaliya a wadannan Jihohin.