A Najeriya, a yau a ke wani taro na 'yan sanda

A Najeriya, a yau ne ma'aikatar kula da ayukan 'yan sanda ta kasa zata soma wani zama na musamman a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom domin tattaunawa akan matsalolin tsaro a kasar.

Taken taron dai shine kalubalen samar da tsaro a karni na ashirin da daya a tsari irin na demokradiyya.

An shirya wannan taron ne domin manyan jami'an 'yan sanda masu rike da mukamin mataimakin kwamishina zuwa sama, wanda sune gaba kadan zasu amshi ragamar gudanar da ayukan 'yan sandan Nijeriya.

Ana saka ran cewa wadanda aka shirya taron domin su, zasu kara fahimtar mahimmancin aikin dan sanda, da kuma kulla alaka mai kyau tsakaninsu da al'ummar gari da kuma 'yan jarida.

An kuma shirya wannan taron ne a daidai lokacin da Najeriya ke cigaba da fuskantar matsaloli na rashin tsaro da keta doka da oda, wanda mafi yawan wannan nauyi ne da ya rataya akan 'yan sanda da su tabbatar komai ya tafi kamar yanda ya kamata.