An fara kada kuri'a a Amurka

Image caption Tutar Amurka

Amerikawa sun fara kada kuri'a a zaben rabin wa'adin mulki wanda ake kira Mid-term Election a Turance, inda jam'iyyar shugaba Obama ke fuskantar babban kalubale.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa mai yiwuwa jam'iyyar Democracts mai mulki ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar Wakilai.

Ana gudanar da irin wannan zaben ne bayan shekaru biyu da zaben shugaban kasa. Har ila yau za a zabi gwamnonin jihohin kasar guda 36.

Kuma wannan zaben shi ne ke zama zakaran gwajin dafi akan irin farin jini ko akasin haka da jam'iyya mai mulki ta samu a wajen al'ummar kasa.

Zaben dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Obama ke fuskantar kalubalen tattalin arziki da rashin aiyukan yi da kuma batun tsaro, abinda kuma hakan a cewar masu lura da al'amuran siyasa zai iya zama cikas ga gagarumin rinjayen da jam'iyyar Democrat ke da shi a majalisar dokokin kasar.

Kuma wannan zaben shi ne zai auna irin nasarori ko sabanin haka da Shugaba Barrack Obama ya samu akan alkawarurrukan da ya yi a lokacin yakin neman zabe, kafin ya zama shugaban kasa.