An kashe mutane 52 a wata Mujami'a a Iraqi

An kashe mutane 52 a wata Coci a Iraqi
Image caption An dade ana kai hare-hare makamantan wannan a Iraqi

A kalla mutane 52 ne aka kashe bayan da jami'an tsaro suka kusta kai cikin wata cocin Katolika a birnin Baghadaza domin kwato mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Mataimakin ministan cikin gida na Iraqi Hussein Kamal, ya ce an kashe shida daga cikin maharan tare da wasu jami'an 'yan sanda.

A kalla mutane 100 ne a cikin majami'ar ta 'Our Lady of Salvation' inda suke bautar Kiristanci.

Rahotanni sun ce maharan sun nemi a saki wani dan kungiyar al-Qaeda da mahukunta ke tsare da shi.

Wani gidan talabijin a Iraqi al-Baghdadiya, ya ce daya daga cikin maharan ya shaida masa cewa su 'ya'yan kungiyar Islamic State of Iraq ne, wacce ita ce tushen kungiyar al-Qaeda a Iraqi.

Sai dai wasu rahotanni sun ce maharan ba 'yan Iraqi ba ne, Larabawa ne 'yan kasashen waje.

'Limamin aka fara kashewa'

Mazauna yankin Karada inda aka kai harin, sun ji karar fashewar wasu abubuwa da magariba, kafin daga bisani a fara musayar wuta.

'Yan sanda suka ce an fara kai hari ne kan kasuwar hannin jari ta kasar, sannan maharan suka kwace ginin cocin wacce ke kan hanya inda suka fara kashe wasu daga cikin masu gadin wurin.

Wakilin BBC Jim Muir da ke Baghadaza, ya ce daga dukkan alamu maharan cocin suka nufa tun asali.

Image caption Wasu jama'a da suka iso wurin da abin ya faru domin yin jaje

Wani da abin ya faru agabansa a cikin cocin, ya ce maharan "sun shiga dakin bautar inda nan take suka kashe limamin". Mutumin wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce an tara jama'a a cikin wani daki, inda aka nada musu duka.

An yi curko-curko a lokacin da jami'an tsaro suka zagaye ginin da jiragen yaki masu saukar ungulu.

Maharan sun tattauna da mahukunta ta wayar salula, inda suka nemi a saki wani fursunan al-Qaeda da aka kama, da kuma wasu mata musulmai da suka ce wata coci a Masar na tsare da su.

Sai dai tattaunawar ta wargatse, abinda yasa jami'an tsaro suka afkawa ginin, a cewar wakilinmu.

Makwaftan wurin suka ce sun ji fashewar wasu abubuwa biyu a cikin cocin. An yi zargin maharan sun tada gurnetin da suke dauke da ita, sannan suka tada bama-baman da ke jikinsu.

An kama wadanda ake zargi

Ministan tsaron Iraqi Abdul-Qadr al-Obeidi, ya ce jami'an tsaro sun fuskanci ginin ta kasa da kuma sama.

"Mun yanke shawarar kai hari ta sama da kasa, domin ba za mu tsaya muna kallo 'yan ta'adda su kashe 'yan uwanmu Kiristoci da ke bauta ba."

Wata majiya ta tattabar da cewa mutane 56 ne suka jikkata a wannan lamari.

"Farmakin ya yi nasara. An kashe dukkan maharan. Kuma yanzu muna tsare da sauran wadanda ake zargi," in Mista Obeidi.