Ana kidayar kuri'un raba gardama a Nijar

Janar Salou Djibo, Shugaban mulkin sojan Nijar
Image caption Janar Salou Djibo, Shugaban mulkin sojan Nijar

A jamhuriyar Nijar ana cigaba da kidayar kuri'u, bayan zaben raba gardamar da aka gudanar jiya a kasar, a kan wani sabon kundin tsarin mulki.

Kamar yadda hukumar zaben kasar mai zaman kanta, CENI ta bayyana, kawo yanzu kundin tsarin mulkin ya sami karbuwa da kashi 90 cikin 100 a wasu yankunan kasar.

Masu zabe kimanin miliyan shida da dubu dari bakwai ne suka cancanci jefa kuri'ar, domin amincewa ko kuma watsi da sabon kundin tsarin mulkin, wanda zai share fagen sauran zabubukan da za a gudanar a Nijar din a nan gaba.

Rahotanni sun ce mutane da yawa ba su fita zaben ba.