Bamabai sun kashe mutane da dama a Bagdaza

Janaza a Bagdaza
Image caption Har yanzu ana faman neman zaman lafiya

An samu wasu jerin tashin bama bamai a birnin Bagadaza, wanda ya kashe akalla mutane talatin, tare da jikkata wasu mutane saba'in da biyar.

Fashewar bama-bamai goma a lokaci guda, wadanda suka hada da bama baman da aka dasa a gefen titi, da na mota da ma gurnetin da ake harbawa, sun fada kan yankuna da dama ne na 'yan Shi'a a duk fadin birnin Bagadaza.

Da marecen yau Talata ne aka kai hare haren, sa'o'i bayan jana'izar sama da mutane hamsin da aka kashe a wani cocin da a kai garkuwa da shi ranar Lahadi.

Wakilin BBC ya ce jami'an tsaro sun ce yawancin bamabaman sun tashi ne a wuraren da ake yawan hada hada kusa da shaguna, da kasuwanni da wuraren shan shayi.